NURUN ALA NUR“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMASAHABBAI”05( Dr. Mansur Sokoto)

NURUN ALA NUR“BAN SAKI AHLULBAITI BA NA KAMASAHABBAI”05( Dr. Mansur Sokoto).

Advertisements

Isar da sokon musulunci insha Allah

Assalamu alaikum ‘yan uwa abokan arziki alhamdulillah Allah ya bamu nasarar bude wannan shafi sabo tunatar da ‘yan uwa a musulunci dama wanda ba musulmiba sabo ya fahinci addinin islama ba tareda son zuciya ba insha Allah muna fatar Allah ya sanya albarka a wannan nasiha tamu Allah yasa zamuyishine domin shi Azza-wajAllah muna baran addu’arku ta alheri kuma muka kara cewa Allah ya zaunar da kasa tamu nigeria da duniya baki daya amin wassalamu alaikum.

YADDA AKE KARƁAN AURE DA BAYARWA A MUSULUNCI

YADDA AKE KARƁAN AURE DA BAYARWA A MUSULUNCI Menene sharuɗan ɗaura aure , kuma yaya tsigar take a musulunci Aure yana tabbata ne idan aka cika sharuɗa guda  6 :-

1.    A Samu Ma’aurata Guda 2 Na Miji Da Mace Waɗanda Ya Halatta A Ɗaura Musu Aure A Shari’ar Musulunci, Kuma Sun Amince Su Auri Juna.

2.    Waliyyin Mace: Mace Wanda Zai Bayar Da Auren Ta.

3.    Miji Ko Wakilin Miji: Miji Ya Karɓi Aurenshi Ko Wakilinshi Ya Karɓa Mishi A Madadin Miji.

4.    A Kalla Shaidu Guda 2 Waɗanda Zasuyi Shaidar Auren A Tsakanin Ma’aurata.

5.    Sadaki: Za’a Iya Bayar Da Sadaki Duka, Ko Wani Abu Daga Cikin Kafin Ɗaurin Aure, Ko Ranar Ɗaurin Aure, Ko Kuma Bayan Ɗaura Aure.

6.    Tsigar Karɓa Da Bayar Da Aure:  Misali: Indai Miji Ne Zai Karɓi Aurenshi Da Kanshi Sai Yace:- Ina Neman Auren ‘Yar Ka Binta A Wurinka ! Sai Waliyyin Mace Yace:- Na Aurar Maka Da ‘Ya Ta Binta !. In Dai Kuma Mahaifin Miji Ne Zai Karɓa Wa Ɗanshi Aure Shi Kuma Ga Abinda Zaice:- Ina Nema Wa Ɗana Zaidu Auren ‘Yarka Binta A Wurika. Ko Kuma Miji Ya Wakilta Wani Don Ya Karɓa Mishi Aure Shi Wakilin Sai Yace:- Ina Wakiltan Zaidu Wajan Nema Mishi Auren ‘Yar ka Binta A Wurinka. Anan Sai Waliyyin Mace Yace: Na Baiwa Zaidu Auren ‘Yata Binta.Wannan Fa Duka Indai Ya Kasance Mahaifin Mace Ne Yake Bayar Da Auren. Amma Indai Baban Macen Ya Wakilta Wani To Anan Sai A Cire Kalmar ‘Yarka, Misali  Sai Yace: ina neman auren binta a wurinka,ko ace: Zaidu yana neman auren binta a wurinka. Shi kuma sai yace: Na Baiwa Zaidu Auren Binta. Indai Aka Kammala Tsigar Daidai, Aure Ya Kullu Daram Sai Kowa Ya Tashi Ya Tafi. Tsigar Aure Takanzo Da Lafazi Kamar Haka: Na Aurar Maka, Ko Kuma Na Mallaka Maka, Ko Kuma Na Halatta Maka Ita. Amma Duk Lafazin Da Zai Iya Nuni Da Cewa Na Bayar Na Karɓa Ya Halatta Ayishi Da Ko Wani Irin Yare Ne A Duniya. Kuma Ya Kamata Mutane Su Sani Cewa Dole Ne Wakilin Miji Yasan Sunan Ango, In Kuma Be SaniBa ya Zama Wajibi A Tsayar Da Ɗaurin Auren Har Sai Yaje Wurin Ango Ya Gaya Mishi Sunanshi Sannan Ya Dawo Ya Tabbatar Wa Mutane Asalin Sunan Wanda Yake Wakilta Kafin A Ɗaura Aure Itama Mace Haka Za’ayi Insha Allah. Wallahu Ta’ala A’alam.

KUSKURE WAJAN BAYAR DA AURE DA KARƁA:-

1. Wakilin Ango Indai Yazo Yana Karɓan Aure Sai Kuji Yace Na Karɓi Auren Binta, To Wannan Babban Kuskure Ne Har Indai Akayi Haka  Aka Tashi Daga Wannan Ɗaurin Auren  To Aure Be Kullu Ba Tsakanin Miji Da Mata,  Kawai Ya Kullu Ne Tsakanin Wakilin Ango Da Mace.

2. Waliyyin Mace Sai Kuji Yace Wa Wakilin Ango, Na Baka, Ka Bashi Auren Binta. To Wannan Ma Kuskure Ne Babba. Inda Kazo Bayar Da Aure Karka Sanya Wani A Tsakani, Abinda Ake Bukata Kwaya Ɗaya Shine Na Baiwa Zaidu Auren Binta Kai Tsaye Zaka Sadar Da Auren Zuwaga Meshi. Da dai saura kura kurai masu tarin yawa. Wallahu Ta’ala A’alam.

AKWAI WASSU FURUCI A CIKIN SHARI’AR MUSULUNCI FURTASU DA WASA TO DA GASKE NE:-

1. Aure: In Kace Na Baka Sai Ɗayan Yace Na Karɓa, Kuma Kana Nufin Da Wasa Kakeyi To Anan Aure Ya Kullu Daram Koda Kuwa Minti 5 Da Haihuwanta, Abinda Zai Warware Wannan Aure Kawai Shine Ya Saketa Sannan Kuma Taci Rabin Sadaki Dole Kuma Ya Bayar. In Kuma Ba haka Ba Matarshi Ce.

2. Sakun Mace: Ko Da Wasa Kace Ka Sake Matarka Daga Baya Kace Ai Wasa Kakeyi To Ya Zama Gaske Sai Dai In Akwai Sauran Igiya Sai Ka Dawo Da Ita. Indai Babu Kuma To Ta Tafi Kenan In Kuma Kayi Taurin Kai Ka Zauna Da Ita A Haka Zakuyita Zina Ne Kawai Kuna Haihuwan Shegu Allah Ya Sauwake.

3. Kome: Indai Kace Na Komar Da Matana Amma Kace Da Wasa Kakeyi To Ya Zama Da Gaske Saidai Ka Sake Sabon Saki.saboda haka kowa yasan irin abinda zai fito daga bakinshi.Allah yasa mu gane gaskiya, mu fahinceta sannan muyi aiki da ita amin.Allah ya baku hakuri. Wallahu Ta’ala A’alam.MUNA MARABA DA GYARE GYARE INSHA ALLAH. daga ‘Yan uwa a musulunci.  08066968935.